Home » Ziyarar Muhasa Talabijin da Rediyo Zuwa Gidan Tarihi na jihar Maradi Dake Jamhuriyar Nijar.

Ziyarar Muhasa Talabijin da Rediyo Zuwa Gidan Tarihi na jihar Maradi Dake Jamhuriyar Nijar.

by Suraj Na iya Kududdufawa
0 comment

A watan Satumba na shekarar da ta gabata ta 2024 gidan talabijin da rediyo na Muhasa dake a kasar Najeriya ya kai ziyarar aiki zuwa sassan jamhuriyar kasar Nijar.

Jihar Maradi na daya daga cikin jihoshin kasar ta Nijar kuma ita ake yiwa lakabi da cibiyar kasuwanci ta kasar Nijar, wannan gidan talabijin na Muhasa ya kai ziyara gidan tarihi na jihar ta Maradi wato (IRSH).

A yayin kai ziyarar zuwa IRSH Muhasa Talabijin da Rediyo ta tattauna da Daraktan gidan tarihi na Maradi inda ya bayyana abubuwa da dama, daga ciki har da shi kansa tarihin wannan gidan tarihi na jihar.

An kafa wannan gidan tarihi na jihar ta Maradi tun a shekarar 1944, kuma wannan gidan tarihi ya kasance yana ajiye kayan tarihi kama daga kasar Najar da sauran sassan kasashe, a takaice ma dukkanin tarihin da mutum yake nema a duniya idan yaje IRSH zai same shi.

Sannan wannan gidan tarihi daga kasashe daban-daban na duniya ana zuwa kama daga kasar Amurka da Ingila da Faransa har ma daga kasar China, su kan zo su kwashe kwanaki domin samun tarihi.

Daraktan ya sake bayyanawa Muhasa rediyo da talabijin cewar a wannan gidan na IRSH akwai tsangaya har kala biyar.

Akwai tsangaya wadda take bayar da tarihi tsantsa, akwai tsangaya mai bayar da tarihin ma’adanai da ake hakosu a can kasa da sauran tsangayoyi.

Sannan akwai littatafai sosai da sosai a gidan tarihin na jihar Maradi wanda al’umma suke yawan zuwa ake basu suna gudanar da bincike.

Akwai kuma hotunan wasu daga cikin tsofaffin shuwagabannin kasar Nijar a wannan gida na tarihi kamar yadda ake gananinsu reras.

Bugu da kari an rika kafa gidan tarihi na Maradi kana aka zo aka gina jami’a a shekarar 1974, amma mafiya yawan dalibai sukan ziyarci IRSH domin sanin wasu abubuwa da suka shigemusu duhu.

Wadannan kuma hotunan wasu abubuwan tarihi ne da mayaka ko masu kare kai suke amfani dasu musamman a shekarun baya kamar yadda suma ake kallonsu a jikin hoto a wannan gidan tarihi dake jihar ta Maradi.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?