Ɗan takarar gwamnan na jam’iyyar Labour Party a jihar Adamawa, Umar Mustapha Otumba ya sanar da janyewa ‘yar takarar gwamna, kuma mace tilo a ƙasar nan sanata Aisha Ahmad Binani tare alƙawarin mara mata baya.
Wannan na zuwa ne ƙasa da sati ɗaya da zaɓen gwamnoni da za a gudanar a Kano, inda Umar Mustapha ya bayyana cewa yana sane da cin dunduniyarsa da jam’iyyarsa ta Labour Party ke yi tare da roƙon magoya bayansa da su mara wa ‘yar takarar APC Aishatu Binani a zaɓen da za gudanar a ranar 11 ga watan da muke ciki.
Umar Mustapha ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi a gaban jiga-jigan jam’iyya ta APC, inda ya bayyana cewa ya yanke shawarar mara mata baya ne saboda ƙarfin guiwar da yake da ita a kanta na son da take da shi wajen hidimta wa al’ummar jihar.
A ya yin da take jawabi, Aishatu Binani, ta yaba wa ɗan takarar bisa ƙarfin guiwar da ya nuna tare da kira ga sauran ‘yan takara da su yi koyi da irin kishin da ya nuna.
Tun a baya dai, Aishatu Binani ce ta yi nasara a kan shi ɗan takarar a zaɓen cikin gida da aka yi na Jam’iyyar APC kafin sauyin sheƙarsa zuwa Labour Party wacce ta ba shi takarar gwamna.