• Home  
  • Kano: Gini Ya Rufta Kan Mutane 16 Ciki Har Da Yara Shida
- Babban Labari

Kano: Gini Ya Rufta Kan Mutane 16 Ciki Har Da Yara Shida

Akalla mutane 16 ne gini ya rufta a kansu a yankin Dan Dishe, Kwanar Yashi, da ke Ƙaramar Hukumar Fagge a Jihar Kano Rahotanni sun ce jami’an ceto sun samu nasarar fitar da mutane 13 daga cikin ginin da ransu, ciki har da yara shida. Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano ta tabbatar da faruwar […]

Akalla mutane 16 ne gini ya rufta a kansu a yankin Dan Dishe, Kwanar Yashi, da ke Ƙaramar Hukumar Fagge a Jihar Kano

Rahotanni sun ce jami’an ceto sun samu nasarar fitar da mutane 13 daga cikin ginin da ransu, ciki har da yara shida.

Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce ginin ya rufta da misalin ƙarfe 4:32 na asubahin ranar Asabar.

A cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar, ta ce jami’an ceto sun garzaya wurin bayan samun kiran neman agaji.

Bayan isarsu wurin, jami’an sun gano cewa wani gini mai girman kusan ƙafa 20 da 30 ya rufta, lamarin da ya rutsa da mutane 16.

Hukumar ta ce an yi nasarar ceto mutane 13 da ransu, ciki har da yara shida, yayin da ake ci gaba da bincike domin gano musabbabin ruftawar ginin

Ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, ba a bayyana ko akwai wasu mutane da suka rasa rayukansu ko suka samu raunuka sakamakon lamarin ba

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000