• Home  
  • Ƙasar Saudiyya Ta Ja Kunnen Masu Ɗaukar Hoto a Lokacin Ibada
- Labarai

Ƙasar Saudiyya Ta Ja Kunnen Masu Ɗaukar Hoto a Lokacin Ibada

Ƙasar Saudiyya Ta Ja Kunnen Masu Ɗaukar Hoto Sanfurin a Lokacin Ibada

Hukumar kula da aikin Haji da Umrah ta Saudiyya ta yi kira ga masu ziyarar ibada da su guji ɗauke-ɗauken hotuna a yayin gudanar da ibada a wurare masu alfarma.

Hukumar ta ce bai kamata masu ziyarar ibadar su ɓige da ɗaukar hotuna ba a maimakon mayar da hankali kan ibadar da ta kai su ƙasar.

Haka kuma hukumar ta gargaɗi masu ɗaukar hotunan da su guji ɗaukar hoton da fuskokin mutane a cikin hoton nasu ba tare da izini ba.

Sannan ta bayyana cewar masu ziyarar ibadar su daina tsayawa don ɗaukar hoto a wuraren da jama’a da dama ke taruwa, domin a cewarta hakan na janyo cunkuson jama’a a wuraren.

A baya-bayan nan dai mutane sun ɓullo da salon ɗaukar hotuna a lokacin ziyarar Umrah ko Aikin Hajji tare da wallafawa a shafukansu na sada zumunta.

Lamarin da wasu malamai ke ganin cewa yawan yin hakan ka iya zama ‘Riya’, abin da kuma a cewar malaman zai iya ɓata wa mutane niyyar ibadar tasu.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000