A jihar Diffa a jamhuriyar Nijar, al’ummomi na kokawa kan yawaitar ayyukan faɗan daba da ƙwacen waya ta hanyar amfani da miyagun makamai.
Hukumomi sun ɗora laifukan a kan mutanen da suka bayyana da baƙi duk da dai wasu ƴan ƙasar su ma na da hannu a cikin miyagun lafiukan.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da ƙungiyoyin da ke ɗauke da makamai da suka haɗa da Boko Haram da sauransu ke zafafa hare-hare da ke haddasa salwantar rayukan jami’an tsaro da na fararen hula.

