• Home  
  • Najeriya Ta Kulla Kawance Da Israila Domin  Yaki Da Rashin Tsaro
- Babban Labari - Labarai

Najeriya Ta Kulla Kawance Da Israila Domin  Yaki Da Rashin Tsaro

Karamar Ministar Harkokin Wajen Najeriya Mrs Bianca Odumegwu-Ojukwu ta jagoranci kulla sabuwar yarjejeniyar da kasar Israila domin yaki da ‘yan taadda da rashin tsaro a kasar. 

Karamar Ministar Harkokin Wajen Najeriya Mrs Bianca Odumegwu-Ojukwu ta jagoranci kulla sabuwar yarjejeniyar da kasar Israila domin yaki da ‘yan taadda da rashin tsaro a kasar. 

Najeriya da kasar Isra’ila sun jaddada aniyarsu na zurfafa hadin gwiwa a muhimman fannoni da suka hada da yaki da ta’addanci, da bayanan sirri, da musayar bayanai, da kuma samar da kudade a fannin tsaro, da horar da jami’an tsaro a kasar. 

Wannan na kunshe a cikin wata sanarwar Karamar Ministar Harkokin Wajen Najeriya Mrs Bianca Odumegwu-Ojukwu, da takwararta ta Isra’ila, mataimakin ministan harkokin waje, Sharren Haskel-Harpaz suka sanya wa hannnu.

Sanarwar ta fito ne bayan wani babban taron da ya gudana a ranar Litinin din da ta gabata a Abuja.

wannan na kunshe a cikin wani labari da jaridar business day ta wallafa.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai