Gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya sha alwashin ɗaukar mataki akan duk wanda aka samu da laifi kan sanadiyyar rasuwar kwamandan rundunar tsaro da ke yaƙi da faɗan Daba da ƙwacen Waya da kuma daƙile shaye-shayen kayan maye ta Anti-Phone Snaching ta jihar Kano, Inuwa Salisu Sharaɗa.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin da ya jagoranci jana’izar marigayin, wanda aka binne shi a maƙanatar Sharaɗa da ke ƙaramar hukumar Birni, a yau Alhamis.
“Yanzu haka likitoci sun dukufa wajen zurfafa bincike domin gano sanadiyyar rasuwar Inuwa, domin an tafi da jinin Marigayin zuwa jihar Legas, kuma na yi magana da kwamishinan Shari’a na Kano, don ya yi abinda ya kamata da zarar an kawo sakamakon binciken, in ji shi.”
A ranar Laraba 29 ga watan Octoba, 2025, ne dai marigayin ya rasu, inda ƴan uwansa su ka alaƙanta hakan da dalilin zuwan jami’an tsaro gidan sa da ke Sharaɗa, domin kama shi, lamarin da firgita shi da su ka yi ya faɗi har daga bisani ya rasa ransa, ko da dai sun bukaci a zurfafa bincike bisa zargin jami’an tsaro da su ke yi a sanadiyyar rasuwar sa, da kuma wani kwamishina a Kano.
Abba Kabir, ya kuma ce duk wanda ba ya son aikin da rundunar ta ke yi, to yanzu ma za ta fara aiki duba da yadda marigayin ya ɗora rundunar akan turba mai kyau na yaƙi da ɓata gari a Kano, domin kuwa tuni ya bai wa yaya ga Inuwa jagorancin rundunar.
Da yake jawabin karɓar sabon muƙamin ɗan uwan marigayin Nura Salisu, ya ce a shirye yake wajen yin aiki tuƙuru domin magance matsalolin faɗan Daba, da kwacen waya da kuma ta’ammali da kayan maye.
Ibrahim Garba Ahmad, shi ne mai magana da yawun rundunar tsaro ta Anti-Phone Snaching a nan Kano, ya ce aikin rundunar yanzu ma za su sanya ɗanba wajen yaƙi da ɓata gari.
- Tinubu Ya Nemi Sabbin Hafsoshin Soja Su Daƙile Sabbin Barazanar Tsaro
- Wasu Yan Majalissar Wakilai Shida Sun Koma APC
Sai dai ya ce akwai buƙatar gwamann Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya sa a zurfafa bincike kan rasuwar Kwamanda Inuwa Salisu Sharaɗa, domin ɗauka mataki na gaba.
Gwamna Abba Kabir, ya kuma haƙurkurtar da jami’an rundunar, da kuma iyalansa, da su yi haƙuri domin za su ƙwatowa marigayin haƙƙinsa, da zarar an kammala bincike, inda ya kuma yi addu’ar Allah ya jikansa.
A yayin jana’izar marigayi Inuwa Salisu Sharaɗa, gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, na tare da sakataren gwamnatin jihar Umar Farouk Ibrahim, da kwamishinoni daban-daban, da kuma mataimakansa da dama, har ma da Dagacin garin Sharaɗa Ilyasu Mu’azu Sharaɗa, da jami’an rundunar ta Anti Phone Snatching, da dai sauransu.

