• Home  
  • An ga watan Ramadan a Najeriya
- Babban Labari - Labarai

An ga watan Ramadan a Najeriya

Hukumomin ƙasar sun sanar da ganin jinjirin watan azumin watan Ramadan na bana, wanda hakan ke nufin za a fara azumin daga gobe Laraba 17 ga watan Fabrairu a ƙasar ta Saudiyya. Shafin Haramain ne ya sanar da haka a kafar X, inda shafin ya ruwaito cewa, “an ga jinjirin wata a ƙasar Saudiyya. Don […]

Hukumomin ƙasar sun sanar da ganin jinjirin watan azumin watan Ramadan na bana, wanda hakan ke nufin za a fara azumin daga gobe Laraba 17 ga watan Fabrairu a ƙasar ta Saudiyya.

Shafin Haramain ne ya sanar da haka a kafar X, inda shafin ya ruwaito cewa, “an ga jinjirin wata a ƙasar Saudiyya. Don haka za a fara azumin wata Ramadan na shekarar 1447 daga gobe,” kamar yadda sanarwar ta nuna.

Tuni dai hukumomi a Najeriya suka buƙaci musulman ƙasar su nemi jinjirin watan a yau Talata 17 ga Fabrairu 2026, wadda ta yi daidai da 29 ga watan Sha’aban 1447AH.

Buƙatar na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da ta fito daga fadar mai alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar.

Sanarwar ta buƙaci Musulmi su fara neman jinjirin watan azumi a wannan rana, tare da umartar duk wanda ya ga watan da ya kai rahoto ga shugaban ƙaramar hukuma ko Dagaci mafi kusa domin a isar da saƙon ga fadar Sarkin Musulmi.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai