• Home  
  • Ƴan sanda sun fara bincike kan mutuwar wanda ake zargi da sokawa matashi Wuƙa a Kano
- Babban Labari

Ƴan sanda sun fara bincike kan mutuwar wanda ake zargi da sokawa matashi Wuƙa a Kano

  Kwamishinan ƴan sandan jihar Kano , CP Ibrahim Adamu Bakori, ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan mutuwar wani matashi da ake zargi da soka wa wani mai suna Yakubu Ƴar-tsohuwa wuƙa a ƙirji, a wani rikici da ya farua tsakaninsu. Kakakin rundunar ƴan sandan jihar, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya bayyana […]

 

Kwamishinan ƴan sandan jihar Kano , CP Ibrahim Adamu Bakori, ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan mutuwar wani matashi da ake zargi da soka wa wani mai suna Yakubu Ƴar-tsohuwa wuƙa a ƙirji, a wani rikici da ya farua tsakaninsu.

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya bayyana cewa rahoton da suka samu daga ofishin ƴan sanda na Hotoro a ranar Lahadi, 31 ga watan Mayun shekarar 2026, ya nuna cewa wasu matasa biyu ne suka samu saɓani, inda ɗaya daga cikinsu ya soka wa wani wuƙa a ƙirji, daga nan ne aka garzaya da wanda ya samu raunin zuwa asibiti domin samun kulawar likitoci.

Sai dai bayan aukuwar lamarin, wasu daga cikin mazauna yankin sun yi wa wanda ake zargi da aikata laifin dukan tsiya, inda ya faɗi magashiyan kuma bayan kai shi asibiti likita ya tabbatar da rasuwarsa.

Kakakin rundunar ƴan sandan ya ce, bayanan da suka samu daga binciken farko sun bambanta da zargin da mahaifin mamacin ya yi,  a wani faifen bidiyo da ya bazu a kafafen sada zumunta, inda ya ce jami’an ƴan sanda ne suka ɗauko ɗansa daga gida kafin daga baya ya mutu.

Bayan bayyanar wannan bidiyo, kwamishinan ƴan sandan jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori , ya bayar da umarnin a miƙa lamarin ga sashen binciken manyan laifuka ɓangaren binciken kisan kai, domin faɗaɗa bincike da gano hakikanin abin da ya faru.

A nasa ɓangaren, mahaifin mamacin ya bayyana cewa lokacin da ya yi wannan magana bai da cikakkun bayanai game da lamarin, ya ce daga baya ya gano cewa ba jami’an ƴan sanda ne suka je gidansa ba,mutane suka yiwa ɗan nasa rubdugu.

Shi kuwa wanda aka soka wa wuƙar, mai suna Yakubu Yar-Tshohuwa, ya ce marigayin ne ya biyo shi, bayan wata taƙaddama da ta shiga tsakaninsu, duk da cewa an yi ƙoƙarin raba su amma yaje ya ɗauko har sai da ya illata shi.

A ƙarshe, rundunar ƴan sandan jihar Kano ta miƙa saƙon ta’aziyya ga iyalan mamacin da ake zargi, tare da kira ga al’umma da su guji ɗaukar doka a hannunsu, su riƙa barin hukumomin tsaro su gudanar da aikinsu bisa tanadin doka.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000