Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya bayyana cewa raba buhunan shinkafa da taliya ba zai taimaka wa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ba a zaɓen 2027.
A cikin wata sanarwa da mai taimaka masa na musamman kan harkokin yaɗa labarai, Phrank Shaibu, ya fitar a Abuja ranar Talata, Atiku ya ce dimokuraɗiyyar Najeriya tana ta raunana sakamakon tattara ƙarfin iko da gwamnatin Tinubu ke yi.
Sanarwar ta ce a daidai lokacin da gwamnoni sama da 30 suka shiga cikin jam’iyyar mai mulki, abin da ake tsammani shi ne buɗaɗɗiyar siyasa da gasa ta gaskiya. Amma abin mamaki da ake gani shi ne gwamnatin tana tsoron hamayya, da tsoron sahihin gasa, da kuma tsoron ’yan Najeriya.
Atiku ya ce duk da cewa gwamnatin Tinubu na da iko kan tsaro da madafun iko da baitul-mali, da kuma goyon bayan wasu sassa na shari’a, har yanzu tana nuna damuwa da hamayya da kuma ’yan ƙasa.
Ya ce: “Gaskiyar ita ce, buhunan shinkafa da Indomie ba za su iya maye gurbin amincewar jama’a ba. Wannan yunƙurin da ake yi na sauya Najeriya ta koma zuwa‘Rice-geria’ ba zai taimaka ba, sai dai ya ƙare da jin kunya.”
Atiku ya yi zargin cewa jam’iyyun adawa sun shiga rikice-rikice da aka ƙarfafa ta hanyar shari’o’i masu rikitarwa, sannan kuma tsarin zaɓe ya ƙara jawo shakku kan adalci.
Ya ƙara da cewa, tsarewar da ake yi wa ’yan adawa suna nuna amfani da ƙarfin gwamnati wajen tsoratar da su da kuma daƙile muryarsu.
Ya ce: “Dimokuraɗiyya da jam’iyya mai mulki ta mamaye kuma ta ci gaba da raunana hamayya, dimokuraɗiyya ce mai rauni. Idan aka ci gaba da wannan tafarki, Najeriya na iya zama ƙasa mai jam’iyya ɗaya a zahiri.”
Atiku ya jaddada cewa yana nan daram wajen ganin Najeriya ta kasance ƙasa da shugabanci yake fitowa daga zaɓin jama’a, ba daga matsin lamba kan cibiyoyi ko rikice-rikicen jam’iyya da aka ƙirƙira ba.
Ya yi kira ga ’yan Najeriya da su gane abin da ke faruwa, yana mai cewa: “Ƙarfi bai kamata ya tara har ya guji lissafi ba. Shugabanci bai kamata ya ji daɗin zama har ya guji gasa ba.
“A 2027, tambayar ita ce: me ya sa gwamnati mai irin wannan iko har yanzu take tsoron zaɓe mai sahihanci? ’Yan Najeriya sun cancanci amsa, kuma sun cancanci zaɓi.”

