ADC ta fitar da sunayen ’yan takarar gwamnanta a jihohi 28
Jam’iyyar ADC ta fitar da sunayen ’yan takararta na gwamna da mataimakin gwamna a jihohi 28 domin tunkarar zaɓen 2027. Jerin ya ƙunshi wasu fitattun ’yan siyasa, ciki har da tsohon ɗan takarar gwamnan Kaduna na PDP, Isa Ashiru, tsohon Ministan Shari’a, Abubakar Malami. Sauran sun haɗa da tsohon ɗan takarar gwamnan Delta, Great Ogboru, […]










