• Home  
  • Wani mummunan hatsarin mota da ya faru a kan babban titin Calabar
- Daga Masu Karatu - Labarai

Wani mummunan hatsarin mota da ya faru a kan babban titin Calabar

Daliban Jami’ar Kuros Ribas uku da ma’aikaci daya sun rasu a wani mummunan hatsarin motaWani mummunan hatsarin mota da ya faru a kan babban titin Calabar zuwa Itu a jihar Kuros Ribas ya yi sanadiyar mutuwar daliban Jami’ar uku da kuma ma’aikacin jami’ar daya.Hatsarin ya faru ne sa’ilin da wata motar bas kirar coaster da […]

Daliban Jami’ar Kuros Ribas uku da ma’aikaci daya sun rasu a wani mummunan hatsarin mota

Wani mummunan hatsarin mota da ya faru a kan babban titin Calabar zuwa Itu a jihar Kuros Ribas ya yi sanadiyar mutuwar daliban Jami’ar uku da kuma ma’aikacin jami’ar daya.

Hatsarin ya faru ne sa’ilin da wata motar bas kirar coaster da ke dauke da daliban ta yi karo da wata babbar motar daukar kaya (tirela), yayin da suke kan hanyar dawowa daga wani aikin hukuma a garin Uyo na jihar Akwa Ibom.

Hukumar jami’ar ta bayyana a ranar Asabar cewa dalibai 24, wadanda akasarinsu mambobin kungiyar dalibai (SUG) ne, hatsarin ya ritsa da su a daren ranar Juma’a a yankin karamar hukumar Odukpani, kamar yadda gidan talabijin na Channels ya ruwaito.

A cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na jami’ar, Onen Ebri Onen ya fitar, makarantar ta tabbatar da rasuwar.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000