• Home  
  • Kotu ta yankewa Mustapha Usha hukuncin kisa kan kashe matashi a unguwar Bambazau
- Labarai

Kotu ta yankewa Mustapha Usha hukuncin kisa kan kashe matashi a unguwar Bambazau

Babbar kotun jihar Kano mai lamba 11 da ke Bompai ta yanke wa Mustapha Hamza, wanda aka fi sani da Usha, hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan samunsa da laifin kashe Abubakar Abba Wajila a unguwar Dambazau a shekarar 2013. An tuhumi Mustapha bisa sashe na 221 na kundin laifuffuka na jihar Kano, bayan zargin […]

Babbar kotun jihar Kano mai lamba 11 da ke Bompai ta yanke wa Mustapha Hamza, wanda aka fi sani da Usha, hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan samunsa da laifin kashe Abubakar Abba Wajila a unguwar Dambazau a shekarar 2013.

An tuhumi Mustapha bisa sashe na 221 na kundin laifuffuka na jihar Kano, bayan zargin hada baki da Janare da wasu matasa wajen aikata kisan.

Tun da farko, an yanke wa Janare hukuncin kisa a shekarar 2018, yayin da Mustapha ya tsere zuwa kudancin Najeriya kafin daga bisani ‘yan sanda su cafke shi.

Lauyoyin gwamnati sun gabatar da shaidu guda biyar a shari’ar. Alkalin kotun, Mai Shari’a Nasiru Saminu, ya bayyana cewa kotun ta gamsu da hujjojin da aka gabatar, don haka ta yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya.

Sai dai lauyan Mustapha, Barista Abdul Ibrahim Umar, ya ce za su nazarci hukuncin domin duba yiwuwar daukaka kara cikin wa’adin kwanaki 90 da kotun bayar ga wanda bai gamsu da hukuncin ba.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai