• Home  
  • Muna kashe N150m duk wata kan samar da ruwa —Gwamnan Gombe
- Babban Labari

Muna kashe N150m duk wata kan samar da ruwa —Gwamnan Gombe

Gwamnatin Gombe ta ce tana kashe kimanin Naira miliyan 150 a duk wata domin tabbatar da samar da tsaftataccen ruwan sha ga al’ummar jihar. Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya ne ya bayyana hakan yayin da yake bayani game da ƙoƙarin da gwamnatinsa ke yi wajen inganta harkar samar da ruwa a birane da karkara. Ya ce […]

Gwamnatin Gombe ta ce tana kashe kimanin Naira miliyan 150 a duk wata domin tabbatar da samar da tsaftataccen ruwan sha ga al’ummar jihar.

Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya ne ya bayyana hakan yayin da yake bayani game da ƙoƙarin da gwamnatinsa ke yi wajen inganta harkar samar da ruwa a birane da karkara.

Ya ce kuɗaɗen na tafiya ne wajen gyara da kula da muhimman kayan aikin ruwa, ciki har da bututan ruwa da suka lalace da kuma na’urorin tace ruwa, domin tabbatar da ci gaba da samar da ruwa mai tsafta.

A cewarsa, gwamnatin jihar ta ɗauki samar da ruwan sha a matsayin ɗaya daga cikin manyan abubuwa da take bai wa fifiko domin inganta lafiyar jama’a da walwalar al’umma.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai