Tsohon gwamnan Kano kuma jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya sanar da zaɓar Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo a matsayin wanda zai yi wa jam’iyyar NDC takarar gwamna a zaɓen 2027.
Kwankwaso ya faɗi haka ne a saƙon da ya wallafa a shafinsa na X inda ya ce Dakta Nasiru Yusuf Gawuna kuma zai nemi kujerar sanata don wakiltar al’ummar Kano ta Tsakiya.
Ya ce an ɗauki matakin bisa gaskiya da biyayya da kuma ƙwarewa – ɗabi’un da har yanzu ginshiƙai ne a ci gaba da haɗin kan jam’iyyarmu da kuma Kwankwasiyya.
Saarwar ta zo ne bayan shafe kwanaki ana tattaunawar sirri a tsakanin mambobin Kwankwasiyya da kuma tuntuɓar manyan ƴan siyasa.
Kwamared Gwarzo ya sauka daga muƙaminsa na mataimaki gwamnan jihar Kano a watan Maris sakamakon rikicin siyasa tun bayan da gwamna Abba Kabir Yusuf ya fice daga NNPP ya koma jam’iyyar APC mai mulki.
