Tag: kwankwaso

Siyasa

Kwankwaso ya caccaki Ganduje

Mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi watsi da kalaman tsohon shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Ganduje, cewa tikitin takarar Peter Obi da Kwankwaso ba zai yi tasiri a Jihar Kano ba. Kwankwaso, yayin wata hira da gidan talabijin na News Central TV, ya ce APC ba ta […]

Babban Labari

Kwankwaso da Dickson sun gana kan rikicin NDC a Kano

Ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya gana da Jagoran Jam’iyyar na ƙasa, Sanata Seriake Dickson, a gidansa da ke Guzape a Abuja ranar Talata. Taron ya samu halartar ɗan takarar gwamnan Kano na jam’iyyar, Kwamared Aminu Abdussalam, da Shehu Wada Sagagi, Nasiru Garo da sauran manyan jagororin NDC. […]

Babban Labari

Ɗan Kwankwaso ya zama ɗan takarar Mataimakin Gwamnan Kano a NDC

Ɗan takarar gwamnan Jihar Kano a jam’iyyar NDC, Aminu Abdussalam Gwarzo, ya zaɓi Mustapha Rabiu Musa Kwankwaso, ɗan Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, a matsayin abokin takararsa na mataimakin gwamna a Zaɓen 2027. Mustapha Kwankwaso, wanda tsohon Kwamishinan Matasa da Wasanni ne a gwamnatin Abba Kabir Yusuf, ya yi murabus daga muƙaminsa, inda ya koma tafiyar […]

Babban Labari

Ɗan Ganduje Ya Sayi Fom Ɗin Takarar Majalisar Tarayya A NDC

Abdulaziz Umar Ganduje, babban ɗan tsohon Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya sayi fom ɗin takarar kujerar Majalisar Tarayya a ƙarƙashin jam’iyyar NDC. Zai tsaya takarar ne a mazaɓar Dawakin Tofa/Tofa/Rimin Gado da ke Jihar Kano. Duk da kasancewar mahaifinsa a jam’iyyar APC, Abdulaziz, ya daɗe yana bin siyasar Kwankwasiyya kuma yana […]

Babban Labari

Kwankwaso ya koma jam’iyyar ADC tare da magoya bayansa

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso ya koma jam’iyyar haɗaka ta ADC tare da magoya bayansa bayan ficewarsa daga jam’iyyar NNPP. An gudanar da bikin komawarsa ne a gidansa da ke Kano, inda shuwagabannin jam’iyyar da dimbin magoya bayansa suka hallara domin tarbar sa. Tsohon gwamnan ya kuma buƙaci magoya bayansa […]

Babban Labari

Kwankwaso ya haɗe da Atiku da Obi don yaƙar Tinubu a 2027

A yau ake sa ran madugun tafiyar Kwankwasiyya kuma Jagoran Jam’iyyar NNPP na Ƙasa, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso zai koma Jami’yyar adawa ADC a hukumance. A ƙarshen mako Kwankwaso ya sanar da ficewarsa daga NNPP, a daidai lokacin da ’yan adawa ke shirye-shiryen da neman tsara lissafin siyasarsu domin ƙwace mulki daga Shugaba Bola Ahmed […]

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai