• Home  
  • Ya kamata gwamnatin Najeriya ta rage farashin man fetur – Sheikh Qaribullah
- Babban Labari

Ya kamata gwamnatin Najeriya ta rage farashin man fetur – Sheikh Qaribullah

Shugaban ɗarikar Ƙadiriyya na Afirka, Sheikh Qaribullah Sheikh Nasiru Kabara, ya buƙaci gwamnatin Najeriya ta duba yiwuwar rage farashin man fetur domin sauƙaƙa wa al’umma matsin rayuwar da suke fuskanta. Shehin Malamin ya bayyana hakan ne ta bakin wakilinsa, Sheikh Abdulgaffar Nasiru Kabara, wanda ya wakilce shi a taron Qadiriyya Media Connect da aka gudanar […]

Shugaban ɗarikar Ƙadiriyya na Afirka, Sheikh Qaribullah Sheikh Nasiru Kabara, ya buƙaci gwamnatin Najeriya ta duba yiwuwar rage farashin man fetur domin sauƙaƙa wa al’umma matsin rayuwar da suke fuskanta.

Shehin Malamin ya bayyana hakan ne ta bakin wakilinsa, Sheikh Abdulgaffar Nasiru Kabara, wanda ya wakilce shi a taron Qadiriyya Media Connect da aka gudanar a birnin Kano.

Ya ce akwai buƙatar gwamnati da masu ruwa da tsaki su yi la’akari da sauƙin da aka samu a kasuwar mai ta duniya bayan cimma yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin Iran da Amurka.

“Akwai buƙatar hukumomi su yi la’akari da sauƙin da aka samu a kasuwar mai ta duniya bayan ci gaban da aka samu na yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin Iran da Amurka, wanda ya taimaka wajen rage fargabar rikici a yankin Gabas ta Tsakiya da kuma saukar farashin mai a kasuwannin duniya,” in ji shi.

Taron Qadiriyya Media Connect wani taro ne da matasa mabiya ɗarikar Ƙadiriyya ke shirya wa a duk shekara, inda mabiya ɗarikar daga sassa daban-daban na Najeriya ke haɗuwa domin tattauna batutuwan ilimi, sada zumunci da sauran al’amuran rayuwa.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai