Mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi watsi da kalaman tsohon shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Ganduje, cewa tikitin takarar Peter Obi da Kwankwaso ba zai yi tasiri a Jihar Kano ba.
Kwankwaso, yayin wata hira da gidan talabijin na News Central TV, ya ce APC ba ta da hujjar sukar tikitin NDC, yana mai jaddada cewa jam’iyyar ta sha kaye a Kano duk da cewa Ganduje ne ke mulkin jihar a lokacin.
Ya ce, “Mun mara masa baya a 2015, amma a 2023 mun kayar da shi. Idan bai iya yin wani abin a zo a gani lokacin yana gwamna ba, me zai iya yi yanzu?”
Martanin na Kwankwaso ya biyo bayan kalaman Ganduje cewa tikitin Peter Obi da Kwankwaso ba shi da ƙarfin siyasa ko shugabanci da zai ba shi nasara a Kano a zaɓen 2027, inda ya bayyana tikitin a matsayin wanda “ya mutu tun kafin fara takara.”
Kwankwaso ya dage cewa tarihin zaɓukan da aka yi a Kano ya nuna APC ba ta da hurumin raina damar tikitin NDC a zaɓen 2027.
