Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta shirya nazari kan ƙorafe-ƙorafen da aka shigar gabanta game da cire sunan Farfesa Isa Ali Pantami da wasu ’yan takara daga jerin sunayen waɗanda za su yi takara a zaɓen 2027.
Majiyoyi a hukumar sun shaida wa Aminiya cewa INEC za ta tattauna kan ƙorafe-ƙorafen a taronta na ranar Alhamis, 29 ga Oktoba.
Tsohon Ministan Sadarwa, Pantami, ya miƙa ƙorafinsa ne ga hukumar bayan cire sunansa da ta yi a matsayin ɗan takarar gwamnan Jihar Gombe na Jam’iyyar PDP.
Har wa yau, hukumar za ta duba sauran ƙorafe-ƙorafen da sauran ’yan takara suka shigar mata waɗanda suka haɗa da na ɗan takarar gwamnan Kano a Jam’iyyar NDC, Kwamred Aminu Abdulsalam Gwarzo da kuma Ladi Adebutu, ɗan takarar gwamnan Jam’iyyar PDP a Jihar Ogun.
Ƙari sun haɗar da ƙorafin Sanata Danjuma Laah, ɗan takarar gwamna a Jihar Kaduna da Sebastine Hon, wanda SDP ta tsayar a matsayin ɗan takararta na gwamna a Jihar Benue.
Haka kuma sai ƙorafin jam’iyyar PDP a Jihar Nasarawa inda ta shigar da ƙorafi kan cire sunan Esson Mairiga, ɗan majalisar dokokin jihar mai wakiltar Lafia ta Arewa, daga jerin sunayen ’yan takarar jam’iyyar da INEC ta fitar.
