Hukumar ’Yan Najeriya Mazauna Ƙasashen Waje (NiDCOM) ta buƙaci mahukuntan ƙasar Mozambique su gaggauta sakin ’yan Najeriya 42 da aka kama a ƙasar ba tare da bayyana takamaiman laifin da suka aikata ba.
Shugabar hukumar, Abike Dabiri-Erewa, ta bayyana damuwa kan lamarin, tana mai cewa kama ’yan Najeriya ba tare da tuhuma ba abin takaici ne kuma ya kamata a sake su ko kuma a gurfanar da su a gaban kotu idan sun aikata wani laifi.
- Abin da ya sa na koma APC – Gwamnan Zamfara
- Iran na ci gaba da luguden wuta kan Isra’ila da sansanonin Amurka
A wata sanarwa da kakakin NiDCOM, Abdur-Rahman Balogun, ya fitar a Abuja ranar Lahadi, Dabiri-Erewa ta ce abin damuwa ne yadda aka kama ’yan Najeriya kaɗai a yayin wani samame da aka kai a wata kasuwar sayar da kayan gyaran motoci.
Ta ce rahotanni sun nuna cewa an bar ’yan kasuwa na wasu ƙasashe da ke wurin, yayin da aka kama ’yan Najeriya kaɗai, lamarin da ta ce na iya nuna wariya ko nuna ƙyama ga ’yan ƙasar.

