• Home  
  • Adadin mutanen da suka mutu a harin ƴanbindiga a Taraba ya kusa 50
- Babban Labari

Adadin mutanen da suka mutu a harin ƴanbindiga a Taraba ya kusa 50

Yan sanda a jihar Tarabar Najeriya sun ce adadin mutanen da suka mutu sakamakon harin da ‘yan fashin daji suka kai wani kauye a jihar ya ƙaru zuwa 48. Ƴanbindiga sun kai hari hari ƙauyen Binnari da ke ƙaramar hukumar Karim Lamido jim kaɗan bayan sallar Juma’a, suna harbin kan mai uwa da wabi, tare […]

Yan sanda a jihar Tarabar Najeriya sun ce adadin mutanen da suka mutu sakamakon harin da ‘yan fashin daji suka kai wani kauye a jihar ya ƙaru zuwa 48.

Ƴanbindiga sun kai hari hari ƙauyen Binnari da ke ƙaramar hukumar Karim Lamido jim kaɗan bayan sallar Juma’a, suna harbin kan mai uwa da wabi, tare da sace kayayyakin abinci da kuma ƙona shaguna da babura.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Victor Mshelizah, ya shaida wa BBC cewa adadin ya ƙaru ne biyo bayan gano ƙarin gawawwaki 23 a jiya Lahadi.

Ya ce binciken ‘yan sanda ya nuna cewa wasu daga cikin waɗanda harin ya rutsa da su sun nutse ne a ruwa yayin da suke ƙoƙarin tserewa maharan, yayin da aka kashe wasu a cikin dazukan da ke kusa da yankin.

Mazauna ƙauyen sun ce maharan sun shiga ƙauyen ne daga jihar Filato da ke makwabtaka da jihar ɗauke da muggan makamai.

Ƙungiyar kare haƙƙin biladama ta Amnesty International ta zargi hukumomi da gaza kare alummomin ƙauyuka daga hare hare ƴan bindiga.

Zuwa yanzu dai babu ƙungiyar da ta ɗauki alhakin harin, sai dai jihar ta Taraba da sauran jihohin Najeriya na ci gaba da fama da hare haren ƴan bindiga da sace mutane domin karɓar kuɗin fansa.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000