Hukumar zabe mai zaman kantan ta kasa ta ta soke sakamakon zaben jahar adamawa tare da gayyatar kwamishinan zaben jahar da kuma wadanda abun yashafa zuwa babban ofishin hukumar dake birnin tarrayya Abuja
Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa ta lura da da wata sanarwa da kwamishinan zaɓeN na jihar Adamawa ya yi wadda ya bayyana sakamakon zaɓen jihar duk da cewa ana kan tattara sakamakon.
Bayyana sakamako zaben yayin da ake tattara sakamako ya saɓa wa tsarin dokar hukumar, kuma ta bai wa baturen zaɓe damar bayyana sakamakon zaɓe ba kwamishinan zaɓe ba.
Wannan ya sa Hukumar zaɓen ta ƙasa ta dakatar da tattara sakamakon zaɓen tare da umartar hukumomi a jihar kan su gaggauta zuwa babban birnin tarayya a Abuja.
Wannan umarni ya fito ne daga bakin jami’in Labarai da Wayar da Kan Al’mma na Hukumar ta ƙasa, Festus Okoye.
Sannan hukumar ta yi alƙawarin fitar da cikakken bayani a kan wannan al’amari.