Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta yi Allah-wadai da kakkausar murya dangane da cin zarafin kwamishinanta, wanda aka yi masa tsirara, sakamakon ayyana wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Adamawa ba bisa ka’ida ba da kwamishinan zaben ya yi a jiya.
Wani faifan bidiyo ya nuna cewa wasu da ba a san ko su waye ba, sun yi wa kwamishinan hukumar tsirara a jihar Adamawa.
Majiyarmu ta rahoto cewa, ga dukkan alamu, matasan sun kama kwamishinan ne bisa zargin cewa shi ne kwamishinan INEC na jihar, Ari Hudu wanda ya sanar da sakamakon zabe ba bisa ka’ida ba.
Da yake mayar da martani kan wannan lamari mai ban takaici, kwamishinan na kasa kuma shugaban kwamitin yaɗa labarai da wayar da kan masu zabe, Barr. Festus Okoye, ya ce Hukumar ba za ta lamunci wannan cin zarafin ba.