AFCON 2025: Nijeriya ta kora Aljeriya gida

Tawagar ƙwallon ƙafa ta Najeriya, Super Eagles ta lallasa abokiyar hamayyarta, Aljeriya da ci biyu da babu a wasan kwata fainal da suka buga na Gasar AFCON ta 2025.

Yanzu Nijeriya ta tsallaka matakin wasan kusa da na ƙarshe, bayan samun nasara da yammacin ranar Asabar.

Victor Osimhen ne ya fara jefa ƙwallo a ragar Aljeriya a minti na 47, bayan dawowa daga hutun rabin lokaci.

A minti na 57 ɗan wasan ƙungiyar Sevilla da ke ƙasar Sifaniya, Akor Adams, ya sake sanya Najeriya a gaba.

Yanzu haka dai Najeriya za ta kara da masu masaukin baƙi, Maroko a wasan kusa da na ƙarshe a ranar Laraba da misalin ƙarfe 9 na dare.

Tawagar ƙasashen biyu su ne kaɗai da suka lashe dukkanin wasanninsu uku a matakin rukuni.

Wasan dai ya ɗauki hankali duba da irin yadda Super Eagles suka tala leda cikin ƙwarewa da nuna salo, lamarin da ya sanya suka mamaye wasan baki ɗaya.

Masu sharhi kan harkar ƙwallon ƙafa na ganin Najeriya za ta iya ba da mamakin a Gasar AFCON ta bana.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *