Kungiyar SHUDLAS tare da kamfanin Moving Image sun kudiri aniyar ci gaba da wayar da kan mutane illar cin hanci.

An bukaci jama’a da kungiyoyin al’umma su dinga bibiyar aiyukan da gwamnatoci ke sanyawa cikin kasafin kudinsu na kowacce shekara, domin samun daidaito da kuma kaucewa al’mundahana yayin gudanar da aiyukan.

Kungiyar masu sauraren shirin wasan kwikwayon, Shugabanci, SHUDLAS wanda kamfanin Moving Image ke gabatarwa ne suka shirya taron, tare da gabatar da makaloli daga hukumomin dake yaki da hanci da rashawa.

Shugaban kamfanin Moving Image, Abdukarim Muhammad, ya bayyana cewa, shirin wasan kwaikwayon Shugabanci, ne ya haifar da kungiyar SHUDLAS, tunda suka fara shirin a shekarar 2018 kuma kungiyar taga dacewar su rungumi harkar yaki da cin hanci da rashawa.

Anasa bangaren shugaban kungiyar SHUDLAS, Kwamared Murtala Sokoto, ya ce yanzu haka kungiyar tana da cikakkiyar rijista kuma son a ci gaba da wayar da kan mutane illar da cin hanci da rashawa ke yiwa al’umma

Mai bada shawara a kungiyoyi daga jihar Borno, Ambasada Mai-Abba Modu, ya bayyana cewa makalolin da hukumomin, ICPC da EFCC da kuma irin tallafin da gidauniyar MacArthur ke bayarwa kwalliya tana biyan kudin salubu.

hukumomin EFCC da ICPC ,sun bayyana cewa cin hanci ko karbar rashawa bai tsaya iya ga ma’aikatun gwamnati ba, ko karkatar da wani kudi da aka tanada dan yiwa jama’a aiki, sunce hatta tursasawa bisa wata dama da wani ya samu don ya basu aiki shima cin hanci ne kuma ana daukar mataki akai.

Taron ya karkare da bayar da lambobin yabo ga MacArthur , Moving Image, CITAD da wasu daga cikin mambobin kungiyar Shudlas.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *