52
Sanata Abdurrahman Kawu Sumaila mai wakiltar Kano ta kudu ya bayyana cewa ana bai wa kowane Ɗan Majalisar Dattawa kimanin Naira miliyan ashirin da ɗaya a matsayin kuɗin gudanar da ofis.
Sanatan ya ce a duk wata suna karban Naira miliyan daya, kudin da idan aka yi yanke-yanke baya wuce Naira dubu dari shida.
Akwai rade-radin Yan majalisar dattijan da na wakilai albashin su wasu makudan kudade ne, to sai dai cikin wata ganawa da ma nema labarai, sanata Sumaila yace duk wata albashin nasu bai taka kara ya karya ba.
Wannan na zuwa ne bayan zargin da tsohon shugaban ƙasa Olesugun Obasanjo ya yi cewa ‘yan Majalisar ne ke yanke wa kansu albashi. Obasanjo ya zargi ‘yan majalisar da wuce gona da iri wajen yanke wa kansu kudin albashi, a jiya dai majalisar ta bakin kakakin ta ta mayar da martani ga tsohon shugaban inda suka bayyana kalaman nasa a matsayin zance mara tushe.