Home » AMFANIN GWAIBA A JIKIN MUTUM

AMFANIN GWAIBA A JIKIN MUTUM

Gwaiba na da sinadarin gyara fata domin tana dauke da sinadaran bitamin A da B da kuma C. Wadannan sinadaran na taimakawa wajen magance matsalar fata. Indan da kullum za ta kasance mai laushi da damshi da kuma kyalli.

by Zubaidah Abubakar Ahmad
0 comment

Masana kiwon lafiya da cimaka sun bayyana gwaiba a matsayin ɗan itacen dake da matukar tasiri wajen gyaran jiki ɗan Adam

Gwaiba na da sinadarin gyara fata domin tana dauke da sinadaran bitamin A da B da kuma C.

Wadannan sinadaran na taimakawa wajen magance matsalar fata.

Masana sun ce cin gwaiba na sa fata ta kasance mai laushi da damshi da kuma kyalli.

Sinadaran da ke cikin gwaiba suna taimakawa wajen kare fata daga kwayoyin cututtuka da dama.

Yawan cin gwaiba na taimakawa wajen fitowar gashin kai.

Gwaiba na dauke da sinadarin folic acid wanda ke taimaka wa mata masu juna biyu.

Yawan cin gwaiba na taimakawa wajen girman jaririn da ke cikin mahaifiyarsa kafin haihuwa.

GaMasana sun ce gnyen gwaiba na ɗauke da sinadarai da suka haɗa da; antioxidants, antibacterial da anti-inflammatory irin su polyphenols, carotenoids, flavonoids da kuma tannins dake da matukar tasiri wurin kawar da wasu cututtuka da dama a jikin dan adam.

Sinadarin Potassium dake jikin ganyen itaciyar gwaiba yana taimakawa wurin daidaita yanayin jinin jikin Dan Adam.

Saboda yana dauke da kusan kashi 80% na ruwa yana kuma dauke da wadataccen sinadarin fiber, sannan yana taimakawa wajen rage kiba.

Za a iya dafa ganyen itaciyar ta gwaiba don yin shayi, wannan shayi ya zama tamkar shayi na gargajiya a kasar Mexico da wasu bangarori na Kudancin Amurka.

A cewar wani rubutu da aka wallafa a Nutrition and Metabolism, masanan sun bayyana cewa mutanen da suke shan shayin ganyen gwaiba suna samun raguwar kitse bayan makonni takwas.

Kasar Japan ta amince da shayin ganyen gwaiba a matsayin daya daga cikin abinci da suke amfani da shi wajen maganin cutar ciwon suga.

A cewar wani rubutu da aka wallafa a Nutrition and Metabolism, shayin ganyen gwaiba yana hana kwayoyin cuta daban-daban da suka chanjawa zuwa carbohydrate ta hanyar narkewa su zama glucose.

A cewar masanin ilimin abinci mai gina jiki na Bangalore Dr. Anju S, ya ce gwaiba na taimakawa wajen bunkasa garkuwar jiki,” hakan ya sanya yake rage barazanar kamuwa da cututtuka daban-daban.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?