Babban Sufeton ‘Yan Sandan Najeriya Kayode Egbetokun ya ce jami’ansa ba masu zanga-zangar tsadar rayuwa suka kama ba a lokacin da aka gudanar da ita a watan Agusta.
Kayode Egbetokun ya ce, masu ƙoƙarin lalata dukiyoyin al’umma da na gwamnati sika kama ba masu zanga zanga-zanga ba.
Babban Sufeton ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a taron da ya yi da shugabannin hukumomin bincikenn ƙwaƙwaf a Abuja.
Egbetokun ya jaddada cewa jami’an su ba wai masu zanga zangar tsadar rayuwa suka kama ba.
“Ana canza maganar abin da ya faru, kuma ba daidai bane, zai zama rashin dattaku idan aka ce yara 76 muka kama,” a cewar Sufeton.
Bayyanar faifan bidyon wasu da ake ganin basu kai shekara 18 ba a gaban kotu a matsayin wadanda hukumar ‘yan sandan Najeriya ke tuhuma da lalata dukiyoyin gwamnanti da na daidaikun mutane lokacin zanga-zangar tsadar rayuwa ya tayar da hankalin jama’ar Najeriya.