• Home  
  • Aminu Abdussalam ne ɗantakararmu na gwamna a 2027 – Kwankwaso
- Babban Labari

Aminu Abdussalam ne ɗantakararmu na gwamna a 2027 – Kwankwaso

Tsohon gwamnan Kano kuma jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya sanar da zaɓar Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo a matsayin wanda zai yi wa jam’iyyar NDC takarar gwamna a zaɓen 2027. Kwankwaso ya faɗi haka ne a saƙon da ya wallafa a shafinsa na X inda ya ce Dakta Nasiru Yusuf Gawuna kuma zai nemi […]

Tsohon gwamnan Kano kuma jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya sanar da zaɓar Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo a matsayin wanda zai yi wa jam’iyyar NDC takarar gwamna a zaɓen 2027.

Kwankwaso ya faɗi haka ne a saƙon da ya wallafa a shafinsa na X inda ya ce Dakta Nasiru Yusuf Gawuna kuma zai nemi kujerar sanata don wakiltar al’ummar Kano ta Tsakiya.

Ya ce an ɗauki matakin bisa gaskiya da biyayya da kuma ƙwarewa – ɗabi’un da har yanzu ginshiƙai ne a ci gaba da haɗin kan jam’iyyarmu da kuma Kwankwasiyya.

Saarwar ta zo ne bayan shafe kwanaki ana tattaunawar sirri a tsakanin mambobin Kwankwasiyya da kuma tuntuɓar manyan ƴan siyasa.

Kwamared Gwarzo ya sauka daga muƙaminsa na mataimaki gwamnan jihar Kano a watan Maris sakamakon rikicin siyasa tun bayan da gwamna Abba Kabir Yusuf ya fice daga NNPP ya koma jam’iyyar APC mai mulki.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000