Alkaluman wadanda guguwa ta kashe a Amurka ya karu zuwa mutum 29 dai dai lokacin da kakkarfar iskar ke ci gaba da tunkara wasu sassan kasar bayan tafka barna a yankunan kudanci da gabashin kasar.
Jihar Tennessee day ace daga cikin jahohin da kakkarfar guguwar ta yi wa mummunar illa, ta sanar da mutuwar mutane 7 gabanin karuwar adadin zuwa 12 bayan da iska ta tumbuke wata bishiya ta fada kan wani gida tare da kisan kananan yara 2 da wani magidanci 1 a Menphis.
Kakkarfar guguwar wadda ta faro tun a juma’ar da ta gabata ta yi mummunar barna a sassa daban daban bayan rushe tarin gidaje wasu kuma ta kwaye rufinsu tare da jijjige tarin bishiyoyi.
Can a jihar Mississippi inda guguwar ke yin waiwaye mako guda tsakani bayan faruwar ta watan jiya da ta kashe mutane 26, a yanzu haka ma kakkarfar iskar ta sake kisan mutanen da yawansu ya kai 17, idan an tattara alkaluman barnar da ta yi a makwabta da suka kunshi jihohin Arkansas da Alabama da Indiana baya ga llinois a yammacin Amurka da kuma Delaware.
Alkaluman jami’an agaji sun ce kakkarfar guguwar ta raunata tarin mutane da yanzu haka ke karbar kulawa gaggawa a asibitoci.
Kakkarfar guguwar wadda ke tafe da wata irin iska hade da ruwan sama a wasu yankunan bayanai na nuna cewa akwai yiwuwar ta sake yiwa wasu yankuna na kasar komai duk da lafawarta a safiyar yau.