Shugabannin Kasashen duniya da Sarakuna da kuma fitattun mutane sama da 2,300 suka halarci bikin nada Sarki Charles na III a matsayin wanda ya maye gurbin marigayiya Elizabeth ta biyu wadda ta rasu watanni 8 da suka gabata.
Da misalin karfe 12 na rana shugaban mabiya darikar Anglican, Archbishop Justin Welby ya dora hular zinare wadda ke zama hular mulki akan Sarki Charles a bikin da shi ne irinsa na farko tun bayan wanda aka yi a shekarar 1953.
A wajen dakin taron kuwa, an yi ta harba bindigogi ne a fadin kasar da kuma a kan teku, tare da kada kararrawa a mujami’un da ke birnin London.
Sai dai kafin gudanar da bikin dai jami’an ‘yan sandan birnin London sun kama tarin masu zanga zanga wadanda ke adawa da masarautar da kuma korafi akan irin makudan kudaden da ake kashe mata.
Wasu daga cikin masu zanga zangar sun baje rubuce rubucen dake bayyana cewar, ‘wannan ba Sarkinmu bane’.