• Home  
  • An kama ɗan shekaru 80 da wasu 7 kan kisan shugaban MACBAN na Benuwai
- Babban Labari

An kama ɗan shekaru 80 da wasu 7 kan kisan shugaban MACBAN na Benuwai

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Benuwai, ta kama wani tsoho mai shekaru 80 da wasu mutum bakwai kan zargin hannunsu a kisan shugaban ƙungiyar Miyetti Allah (MACBAN) na jihar, Alhaji Ardo Risku Mohammed, da wani mutum mai suna Yakubu Isa. An kashe Mohammed da Isa ne a ranar 1 ga watan Yuli, 2026. An kai musu […]

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Benuwai, ta kama wani tsoho mai shekaru 80 da wasu mutum bakwai kan zargin hannunsu a kisan shugaban ƙungiyar Miyetti Allah (MACBAN) na jihar, Alhaji Ardo Risku Mohammed, da wani mutum mai suna Yakubu Isa.

An kashe Mohammed da Isa ne a ranar 1 ga watan Yuli, 2026.

An kai musu hari yayin da suke kan hanyarsu ta komawa gida bayan sun halarci wani taron tsaro da rundunar ’yan sanda ta shirya a Ƙaramar Hukumar Ohimini da ke Jihar.

Tun bayan faruwar lamarin, ’yan sanda sun kama wasu mutum 10, daga bisani kuma aka ƙara kama wasu da ake zargi.

Sabbin waɗanda aka kama sun haɗa da Chief Morgan Ejaga, Chief Moses Anteyi, Chief John Ogli, Chief Yawuhu Adaji, Sylvester Ajonye mai shekaru 80, Aba Alexander Uloko, da Fidelis Iduma.

Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, DSP Udeme Edet, ta ce an samu nasarar kama su ne sakamakon bayanan sirri da kuma binciken da jami’an tsaro suka gudanar.

Ta bayyana cewa suna ci gaba da bincike, kuma duk wanda aka gano yana da hannu kai-tsaye a kisan zai fuskanci hukunci bisa doka.

Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Benuwai, CP Cletus Nwadiogbu, ya buƙaci jama’a su kwantar da hankali kan lamarin .

Sannan ya nemi su ci gaba da bai wa jami’an tsaro bayanan da za su taimaka wajen gano waɗanda suka aikata laifin.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000