• Home  
  • EFCC ta gurfanar da Bello Bodejo kan zargin badaƙalar kuɗi
- Babban Labari

EFCC ta gurfanar da Bello Bodejo kan zargin badaƙalar kuɗi

Hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin ƙasa ta’annuti a Najeriya (EFCC), ta gurfanar da shugaban ƙungiyar Fulani ta Miyetti Allah Kautal Hore na ƙasa, Bello Bodejo bisa zargin hada-hadar kuɗi da ta wuce ƙima har dala miliyan 2.63. An gurfanar da shi ne a babbar kotun tarayyar Najeriya da ke Abuja ƙarƙashin mai […]

Hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin ƙasa ta’annuti a Najeriya (EFCC), ta gurfanar da shugaban ƙungiyar Fulani ta Miyetti Allah Kautal Hore na ƙasa, Bello Bodejo bisa zargin hada-hadar kuɗi da ta wuce ƙima har dala miliyan 2.63.

An gurfanar da shi ne a babbar kotun tarayyar Najeriya da ke Abuja ƙarƙashin mai shari’a Inyang Ekwo, bisa wasu tuhume-tuhume 12.

EFCC na zargin Bodejo da karɓar tsabar kuɗi dala 200,000 daga Sa’idu Abubakar, tsohon Akanta Janar na Jihar Bauchi, a ranar 21 ga Janairun 2022, abin da ta ce ya zarce iyakar kuɗin da doka ta amince a yi cinikayya ta irin wannan hanya.

Hukumar ta kuma zargi Bodejo da karɓar ƙarin dala 100,000 daga Abubakar a ranar 26 ga Oktoban 2022, da kuma wasu dala 980,000 a wasu mu’amaloli na tsabar kuɗi daban-daban.

Sai dai kotun ta ba da umarnin a ci gaba da tsare Bodejo, kuma zai ci gaba zama a hannun EFCC har sai kotu ta yanke hukunci kan buƙatar belinsa, inda aka ɗage sauraron buƙatar belinsa har zuwa ranar 20 ga watan Yuli.

Bayan karanta tuhumar, lauyan EFCC, Wahab Shittu, ya nemi kotun ta sanya ranar fara shari’ar tare da ci gaba da tsare wanda ake ƙarar.

Sai dai lauyan Bodejo, Ahmed Raji, ya sanar da kotun cewa tuni sun shigar da buƙatar beli, inda ya nemi a saurari buƙatar.

Bodejo dai ya musanta dukkan tuhume-tuhumen da ake masa.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000