• Home  
  • An kashe wutar da wasu gungun yan daba suka kunna a unguwar Rijiya Biyu Kano
- Babban Labari - Labarai

An kashe wutar da wasu gungun yan daba suka kunna a unguwar Rijiya Biyu Kano

An sami nasarar kashe gobarar da ake zargi wasu ‘yan daba sun tayar, a Rijiya biyu  layin Bala DPO dake karamar hukumar  Dala anan jihar  Kano, bayan ta kone dukiya mai yawa. Lamarin dai ya faru ne adaren jiya  Talata, lamarin da ya jefa al’ummar cikin zulumi da tashin hankali. Mazaunin unguwar sun bayyana cewa […]

An sami nasarar kashe gobarar da ake zargi wasu ‘yan daba sun tayar, a Rijiya biyu  layin Bala DPO dake karamar hukumar  Dala anan jihar  Kano, bayan ta kone dukiya mai yawa.

Lamarin dai ya faru ne adaren jiya  Talata, lamarin da ya jefa al’ummar cikin zulumi da tashin hankali.

Mazaunin unguwar sun bayyana cewa gungun yan dabar, sun shigo unguwar dauke da makamai, inda suka cinna wa wajen karan suyar Gurasa wuta tare da sanya sara kan mai uwa dawabi.

Ba wannan ne karon fark oba da ake zargin yan dabar na shiga yankin tare da yunkurin tayar da hankalin al’umma, domin a ranakun lahadin da litinin sai da suka shigo musu.

Rahotanni na cewa yan dabar sun saci kayayyaki daga wasu gidaje, sai kawo yanzu rundunar yan sandan jihar Kano, bata fitar da wata sanarwa ba kan faruwar lamarin.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai