Aƙalla ’yan Najeriya 32 ne aka koro su daga Indiya kan zargin su da hannu a kasuwancin miyagun ƙwayoyi.
A ƙarshen watan da ya gabata, ’yan sandan Delhi da na Telangana, sun kama ’yan Najeriya 50 biyo bayan samamen da suma kai wa wata ƙungiyar safarar miyagun ƙwayoyi mai alaƙa da ƙasashen waje.
Ana zargin mutanen da rarraba ƙwayoyi a birane da dama a Indiya, inda suke amfani da kamfanonin bayar da kaya don ɓoye ƙwayoyin da suke safara.
An gano mutanen suna da alaƙa da wani ɗan Najeriya mai suna “Nick,” wanda ake nema ruwa a jallo, kuma ana zargin yana jagorantar wannan ƙungiyar daga Najeriya.
Wasu majoyi sun bayyana cewa yana da abokan aiki aƙalla 100 a Delhi.
Masu bincike sun ce ƙungiyar tana da waɗanda ke aiki a ƙarƙashinta sama da 3,000 a Indiya kuma tana aika manyan kuɗaɗe zuwa Najeriya.
Daga cikin waɗanda aka kama, an koro ’yan Najeriya 32, yayin da wasu bakwai ke fuskantar tuhumar shari’a.
Hukumomi a ƙasar sun ana ci gaba da ce bincike.

