• Home  
  • An samu ƙarancin masu kaɗa ƙuri’a a zaɓen cike gurbi a Kano
- Babban Labari - Siyasa

An samu ƙarancin masu kaɗa ƙuri’a a zaɓen cike gurbi a Kano

Rahotannin da ke fitowa daga jihar Kano sun nuna cewa an samu ƙarancin fitowar mutane zaɓukan cike gurbin wasu ƴan majalisar dokokin jihar biyu. An gudanar da zaɓukan a rumfunan zaɓe 1,014 a faɗin ƙananan hukumomin Ungogo da Municipal. Bayanai sun nuna cewa duk da isar jami’an zaɓe rumfunan a kan lokaci, da dama mutane […]

Rahotannin da ke fitowa daga jihar Kano sun nuna cewa an samu ƙarancin fitowar mutane zaɓukan cike gurbin wasu ƴan majalisar dokokin jihar biyu.

An gudanar da zaɓukan a rumfunan zaɓe 1,014 a faɗin ƙananan hukumomin Ungogo da Municipal.

Bayanai sun nuna cewa duk da isar jami’an zaɓe rumfunan a kan lokaci, da dama mutane sun ƙi fita zaɓukan.

Hukumar zaɓen ƙasar dai ba ta saka sunan jam’iyyar NNPP da ADC da PDP a kan takardar kaɗa ƙuri’a ba.

Kawo yanzu dai babu rahoton wani tashin hankali a zaɓukan.

Jami’an tsaro sun ƙarfafa tsaro a wuraren da ake gudanar da zaɓukan

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000