• Home  
  • An sanya wa’adin kammala sabuwar tashar lantarki a Katsina
- Labarai

An sanya wa’adin kammala sabuwar tashar lantarki a Katsina

Gwamnatin Tarayya ta sanya Maris na shekarar 2027 a matsayin wa’adin kammala sabuwar tashar raba wutar lantarki mai ƙarfin 132/33kv da ake ginawa a Garo, ƙaramar hukumar Mashi, Jihar Katsina. Ministan Lantarki na Najeriya, Injiniya Joseph Olasunkanmi Tegbe ne ya bayyana hakan yayin kaddamar da harsashin ginin tashar wutar lantarkin a ranar Juma’a 23 ga […]

Gwamnatin Tarayya ta sanya Maris na shekarar 2027 a matsayin wa’adin kammala sabuwar tashar raba wutar lantarki mai ƙarfin 132/33kv da ake ginawa a Garo, ƙaramar hukumar Mashi, Jihar Katsina.

Ministan Lantarki na Najeriya, Injiniya Joseph Olasunkanmi Tegbe ne ya bayyana hakan yayin kaddamar da harsashin ginin tashar wutar lantarkin a ranar Juma’a 23 ga watan Oktoba, 2026 a garin na Garo.

Ya ce, aikin wanda kamfanin kula da rarraba wutar na gwamnati TCN ke yi ya ƙunshi tiransifoma 2X60MVA da za su bayar da ƙarfin 120MVA, kwatankwacin 96MW.

Ministan ya ce, an riga an biya diyya ga masu kadarorin da aikin ya shafa, kuma ya buƙaci ɗan kwangilar da ya kammala aikin akan lokaci tare da yin aiki mai inganci.

A yayin ziyarar, Ministan ya kuma ƙaddamar da tiransfoma 2x60MVA a Kankia, tare da duba aikin tashar GIS mai ƙarfin 2x100MVA a Katsina tare da Gwamna Dikko Umaru Raɗɗa.

A jawabin, Gwamna Raɗɗa ya gode wa Shugaba Bola Tinubu bisa amincewa da tashoshi uku a jihar, yana mai cewa zuba jari ne mai muhimmanci ga tattalin arzikin jihar.

A wani gajeren jawabi da ya yi, Gwamna Raɗɗa ya ce, wancan aikin na na’urar hasken wutar lantarki mai aiki da iska ita ma bada jimawa za a cigaba da aikin kammala ta domin gwamnati ta amince da yin haka.

Gwamna Raɗɗa ya yi wa al’ummar jahar albishirin cewa, batun matsalar hasken wutar lantarki da kuma ruwa za su zama tarihi domin tuni ake cikin aikin janyo ruwan madatsar ruwa ta Zobe zuwa wasu ƙananan hukumomin jahar.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai