• Home  
  • APC ta naɗa Masari shugaban babban taronta na ƙasa
- Labarai - Siyasa

APC ta naɗa Masari shugaban babban taronta na ƙasa

Jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya ta maye gurbin gwamnan jihar Imo Hope Uzodinma da tsohon gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari a matsayin shugaban kwamitin babban taronta na ƙasa. Babban sakataren jam’iyyar na ƙasa, Surajudeen Basiru ne ya bayyana haka cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X. Jam’iyyar ta saka ranakun 27 […]

Jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya ta maye gurbin gwamnan jihar Imo Hope Uzodinma da tsohon gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari a matsayin shugaban kwamitin babban taronta na ƙasa.

Babban sakataren jam’iyyar na ƙasa, Surajudeen Basiru ne ya bayyana haka cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X.

Jam’iyyar ta saka ranakun 27 da 28 ga watan Maris na wannan shekarar a matsayin ranakun da za ta gudanar da babban taronta na ƙasa.

Surajudeen Basiru ya ce a yanzu gwamnan jihar Imo da ke kudu maso gabashin ƙasar zai yi aiki a matsayin ma’ajin kwamitin babban taron.

Haka kuma jam’iyyar ta ƙara yawan mambobin kwamitin babban taron daga 73 zuwa 90, domin bai wa masu ruwa da tsaki damar shiga kwamitin.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai