APC ta naɗa Masari shugaban babban taronta na ƙasa

Jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya ta maye gurbin gwamnan jihar Imo Hope Uzodinma da tsohon gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari a matsayin shugaban kwamitin babban taronta na ƙasa.

Babban sakataren jam’iyyar na ƙasa, Surajudeen Basiru ne ya bayyana haka cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X.

Jam’iyyar ta saka ranakun 27 da 28 ga watan Maris na wannan shekarar a matsayin ranakun da za ta gudanar da babban taronta na ƙasa.

Surajudeen Basiru ya ce a yanzu gwamnan jihar Imo da ke kudu maso gabashin ƙasar zai yi aiki a matsayin ma’ajin kwamitin babban taron.

Haka kuma jam’iyyar ta ƙara yawan mambobin kwamitin babban taron daga 73 zuwa 90, domin bai wa masu ruwa da tsaki damar shiga kwamitin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *