Gwamnatin Jigawa Na Asarar Naira Miiliyan 314 Duk Wata Kan Ma’aikatan Bogi 6,348
Rahotanni daga jihar Jigawa na cewa gwamnatin jihar, ta gano ma’aikatan bogi 6,348, yayin tantance ma’aikatan ta.
Rahotanni daga jihar Jigawa na cewa gwamnatin jihar, ta gano ma’aikatan bogi 6,348, yayin tantance ma’aikatan ta.
Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta kama wasu mutane 24 da ake zargin ‘yan daba ne tare da ƙwato muggan makamai a yayin wani sumame da ta gudanar a tun daga ranakun 13 zuwa 16 ga Disamba, 2024.
Wasu ’yan bindiga sun harbe malamin Jami’ar Nnamdi Azikiwe (UNIZIK), Dokta Osita Chinedu, har lahira a daren Litinin a Jihar Anambra.
Gwamnan jihar Kaduna Malam Uba Sani ya mayar wa iyalan tsohon shugaban kasa Janar Sani Abacha filayen su guda 2 da tsohon gwamna Nasir El Rufai ya kwace a lokacin mulkinsa.
Hukumar Rawa Ta Najeriya (National Troupe of Nigeria) a karkashin jagorancin Kaltume Bulama Gana, FSNA, na shirin wani gagarumin taro domin kaddamar da kirkirarriyar fasahar zamani da zimmar karfafawa yara da matasa guiwa wurin kallo da sauraron wakoki, kade-kade da raye-rayen gargajiya.
Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, ta ce ta kai wani samame mafi girma na yini guda a tarihin kafuwar ta kan wasu da ake zargin masu damfara ne ta kafar intanet, inda ta cafke wasu ‘yan kasashen waje 193 da wasu ‘yan Najeriya 599 a Legas.
Shugabannin Ƙungiyar da ke fafutukar haɗe kan magoya bayan ‘yan siyasa a jam’iyyu daban-daban a Jihar Kano da aka yi wa laƙabi da Kwandon Koli ta kawo ziyarar aiki tashar Rediyo da Talabijin na MUHASA.
An wayi gari da hazo a sassan jihar Kano a safiyar Lahadi, inda ba a iya hango wanda ke sama da mita 500.
A ranar Alhamis ɗin da ta gabata ne rundunar sojin Najeriya ta yi wa manyan hafsoshinta 656 ritaya, wadanda suka shafe shekaru 35 a bakin aiki
Farfesa Mahmood Yakubu, Shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), ya ƙaryata jita-jitar da ake yaɗawa cewa ya rasu a wani asibiti da ke birnin Landan.