• Home  
  • Ba don Tinubu ba, da Buhari bai zama shugaban ƙasa ba – Kashin Shettima
- Babban Labari

Ba don Tinubu ba, da Buhari bai zama shugaban ƙasa ba – Kashin Shettima

Mataimakin shugaban Najeriya, Kashin Shettima ya ce ba don taimakon shugaban Najeriya, Bola Tinubu ba, da tsohon shugaban ƙasa, Marigayi Muhammadu Buhari bai samu nasarar shugabancin ƙasar ba. Shettima ya bayyana haka ne a jawabinsa a wajen taron ƙaddamar da yaƙin zaɓen Tinubu domin neman wa’adi na biyu a jihar Kaduna. Shettima ya ce Tinubu […]

Mataimakin shugaban Najeriya, Kashin Shettima ya ce ba don taimakon shugaban Najeriya, Bola Tinubu ba, da tsohon shugaban ƙasa, Marigayi Muhammadu Buhari bai samu nasarar shugabancin ƙasar ba.

Shettima ya bayyana haka ne a jawabinsa a wajen taron ƙaddamar da yaƙin zaɓen Tinubu domin neman wa’adi na biyu a jihar Kaduna.

Shettima ya ce Tinubu ya taimakawa ƴan arewa a lokuta daban-daban domin neman takarar shugabancin ƙasar.

“Ya taimakawa Atiku domin takara a AD, sannan ya taimakawa Nuhu Ribaɗu a AC, sannan kuma ya taimakawa marigayi Muhammadu Buhari a 2015 da 2019.”

Shettima ya ce kasancewar Tinubu ya bayar da gudunmuwa ga ƴan takarar arewa a baya, yanzu lokaci ne da za a mayar da biki.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai