Shugaban Ƙungiyar Jama’atu Izalatil Bid’a Wa’ikamatis Sunnah (JIBWIS), Sheikh Sani Yahaya Jingir, ya musanta zargin nuna wa Kiristoci ƙiyayya.
Sheikh Jingir, ya ce an yi wa kalamansa da ya yi a auren gata da Gwamnatin Jihar Kano ta shirya, mummunar fahimta.
Ya ce ba shi da nufin nuna ƙiyayya ko cin mutuncin Kiristoci da sauran waɗanda ba Musulmai ba.
Kalaman Jingir sun haifar da ce-ce-ku-ce, inda wasu suka ce kalaman na iya raba kan mutane saboda addini.
Da yake jawabi a ranar Lahadi a wani babban taron tattaunawa na ƙasa da aka gudanar a Jos, Sheikh Jingir, ya ce zargin da ake yi na cewa yana ƙin Kiristoci ba gaskiya ba ne.
“Mutane da yawa suna cewa na tsani Kiristoci, amma ba na nuna musu ƙiyayya. Wannan ba gaskiya ba ne. An yi wa kalamaina wata fahimta ta daban,” in ji shi.
Ya bayyana cewa addinin Musulunci yana koyar da Musulmai su nuna ƙauna da kyakkyawar mu’amala ga mabiya wasu addinai.
A cewarsa, Musulunci ya hana Musulmi ya zalunci ko ya yaudari wanda ba Musulmi ba.
Ya kuma ce Annabi Muhammad (S.A.W), ya rayu cikin zaman lafiya da wasu mabiya addinai.
Sheikh Jingir, ya yi kira ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu, gwamnoni da sauran shugabanni da su yi wa kowa adalci, ba tare da la’akari da addini, ƙabila ko jam’iyyar siyasa ba.
Ya ce bai kamata shugabanni su nuna wa mutane bambanci saboda addininsu ko jam’iyyarsu ba.
“Ina kira ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya yi wa Musulmai da waɗanda ba Musulmai ba adalci. Haka kuma shugabanni su yi wa waɗanda ba ‘yan jam’iyyarsu ba adalci,” in ji shi.
Sheikh Jingir, ya kuma ce kowane ɗan Najeriya na da ’yancin zaɓar wanda yake so da kuma kaɗa ƙuri’a ga ɗan takarar da yake so a lokacin zaɓe.
Ya yi kira ga ’yan Najeriya da su rungumi zaman lafiya, haɗin kai da juna, inda ya bayyana cewa ba za a samu ci gaba mai ma’ana ba idan babu zaman lafiya.

