Ba na nuna wa Kiristoci ƙiyayya — Sheikh Jingir
Shugaban Ƙungiyar Jama’atu Izalatil Bid’a Wa’ikamatis Sunnah (JIBWIS), Sheikh Sani Yahaya Jingir, ya musanta zargin nuna wa Kiristoci ƙiyayya. Sheikh Jingir, ya ce an yi wa kalamansa da ya yi a auren gata da Gwamnatin Jihar Kano ta shirya, mummunar fahimta. Ya ce ba shi da nufin nuna ƙiyayya ko cin mutuncin Kiristoci da sauran […]



