• Home  
  • Babban bankin Nijeriya CBN ya ɓullo da sabuwar doka don ƙarfafa tsaron kuɗin jama’a.
- Babban Labari

Babban bankin Nijeriya CBN ya ɓullo da sabuwar doka don ƙarfafa tsaron kuɗin jama’a.

  Babban Bankin Najeriya, wato Central Bank of Nigeria, ya bullo da sabuwar doka domin ƙarfafa tsaron kuɗin jama’a. Daga ranar 1 ga Mayu, 2026, za a takaita yadda ake canza lambar waya da ke haɗe da BVN, tare da ƙara sa ido idan an canza waya da ake amfani da ita wajen banki. Haka […]

 

Babban Bankin Najeriya, wato Central Bank of Nigeria, ya bullo da sabuwar doka domin ƙarfafa tsaron kuɗin jama’a.

Daga ranar 1 ga Mayu, 2026, za a takaita yadda ake canza lambar waya da ke haɗe da BVN, tare da ƙara sa ido idan an canza waya da ake amfani da ita wajen banki.

Haka kuma, za a iya dakatar da BVN na ɗan lokaci idan an zargi wata damfara, yayin da aka sanya shekaru 18 a matsayin mafi ƙarancin yin rajistar BVN.

Ana sa ran wannan mataki zai taimaka wajen hana shiga asusu ba tare da izini ba, musamman idan an canza na’urar da ake amfani da ita. Haka kuma, dokar za ta ƙara tsaurara sa ido kan mu’amalolin da ake zargi.

An ce matakan na da nufin rage damfara da kare kuɗin ‘yan Najeriya.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai