Hukumar da ke yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya ta’annati ta EFCC ta bayyana damuwa kan yadda harkar nan ta damfara ta yanar gizo ta zama ruwan dare a tsakanin ɗaliban jami’o’in ƙasar.
Da yake jawabi a wani taron shugabannin jami’o’i da aka gudanar a Jihar Kano, Shugaban EFCC, Olanipekun Olukoyedo, ya ce a halin yanzu cikin kowane ɗalibai 10 na jami’o’in ƙasar, ba a rasa mutum 6 da ke wannan aika-aikar da ake kira yahoo-yahoo.
Olanipekun ya ce bincike da ayyukan kama masu laifi da hukumar ta gudanar tsawo shekara ɗaya da ta gabata ne suka tabbatar da yadda ɗalibai suka dulmiya a cikin irin waɗannan laifuka.
Olukoyede ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici, yana mai cewa mafi yawan waɗanda ake kamawa a irin waɗannan aika-aikar na damfara ɗalibai ne, har ma wasu na zargin suna lalata tsarin ilimi ta hanyar bai wa malamai cin hanci.
Ya ce wannan matsala na nuna cewa babu wasu kyawawan tsare-tsare a jami’o’i, ciki har da raunin kulawa da rashin ingantaccen tsarin gudanarwa.
Shugaban na EFCC ya kuma buga misali da wani samame da jami’ansa suka kai a Jihar Legas, inda aka kama mutane 792 da ake zargi da alaƙa da wata babbar ƙungiyar damfara ta ƙasashe da dama, inda ya ce da dama daga cikinsu ɗalibai ne.
Kazalika, shugaban EFCCn ya ƙara da nuna damuwa kan yawaitar abin da ake kira “Yahoo Plus”, wato haɗa damfara da wasu al’amura da suka danganci tsafi.
Ya buƙaci shugabannin jami’o’i da su ɗauki matakan gaggawa, ciki har da amfani da fasahar ƙirƙirarriyar basira ta AI wajen inganta tsaro da gano zamba a fannoni kamar albashi, kwangila da sauran harkokin kuɗi.
Ya jaddada cewa duk jami’ar da babu gaskiya wajen gudanar da harkokinta na kuɗi ba za ta iya samar da ƙwararru masu nagarta ba, yana mai cewa mutuncin jami’o’i na da alaƙa kai tsaye da tsaron ƙasa.
Olukoyede ya kuma buƙaci a ƙara horas da ma’aikata a fannoni kamar tsaro na yanar gizo, koyon amfani da na’ura da fasahohin sadarwa na zamani, tare da ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin jami’o’i da hukumomin yaƙi da cin hanci domin daƙile wannan barazana.
