Ministan Ilimi Mallam Adamu Adamu, ya bayyana cewa bai san komai ba a ɓangaren harkokin ilimi a lokacin da shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya naɗa shi ministan ilimi a shekarar 2015.
Adamu, wanda shi ne minista mafi daɗewa a kan kujera, ya bayyana hakan ne a wajen taron bankwana da ya yi da shugabannin hukumomin ma’aikatar a jiya Alhamis.
Ya ce an tilasta masa yin amfani da hikima ta hanyar naɗa wasu farfesoshi na ilimi da sauran nagartattun mutane, tare da kuma taimakon jami’an ma’aikatar ilimi ta ƙasa, don samun damar fara aiki da kuma kawo ci-gaba.
Ministan ya kuma yabawa shugaban ƙasa da ya ga ya cancanta kuma ya ba shi wannan muƙami, duk da cewa a zahiri bai shirya yin irin aikin ba.
Adamu Adamu ya kuma ce sai da ya bai wa Buhari shawara a shekarar 2019 kan ya yi wa majalisar ministocinsa garambawul ta hanyar sauya wasu da waɗanda ake ganin za su fi su yin abinda ya kamata.