Rundunar yan sandan jihar Kano ta ya bawa al’ummar jihar bisa hadin kai da goyon bayan da suke basu a koda yaushe don wanzar da zaman lafiya mai dorewa.
cikin wani sako da kakakin rundunar yan sandan jihar Kano , SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya wallafa a shafin sa na Facebook, ya ce mutane suna basu hadin kai sosai wajen taimakawa yan sanda, musamman bayan takaddamar da Operation Kukan Kura wanda ake ta samun nasara a koda yaushe.
- An Bukaci Gwamnatin Kano Ta Bai Wa Yara Muhimmanci A Kasafin Kudi -UNICEF
- KAROTA Da NDLEA Sun Fara Wayar Da Kai Kan Illolin Shan Miyagun Kwayoyi A Kano
A cewarsa acan baya sun taba kaddamar da Operation Puff Adder wato kan kace Kobo, kuma shima jama’a sun bayar da hadin kai sosai, sai dai ya ce a wannan lokaci hadin kan da ake samu yafi na baya.

