• Home  
  • Bene mai hawa daya da ake ginawa ya rushe a jihar Sokoto
- Labarai

Bene mai hawa daya da ake ginawa ya rushe a jihar Sokoto

  Wani bene mai hawa daya da ake kan ginawa ya rushe a ranar Laraba a kan titin Bauchi da ke cikin birnin Sakkwato. Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, ba a tabbatar da musabbabin rushewar ginin ba, sannan babu cikakken bayani kan ko akwai wadanda suka mutu ko suka jikkata sakamakon lamarin. Hukumomin ba […]

 

Wani bene mai hawa daya da ake kan ginawa ya rushe a ranar Laraba a kan titin Bauchi da ke cikin birnin Sakkwato.

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, ba a tabbatar da musabbabin rushewar ginin ba, sannan babu cikakken bayani kan ko akwai wadanda suka mutu ko suka jikkata sakamakon lamarin.

Hukumomin ba da agajin gaggawa da sauran hukumomin da abin ya shafa ba su fitar da wata sanarwa a hukumance ba.

Sai dai shaidun gani da ido sun ce mutane sun yi tururuwa zuwa wurin da ginin ya rushe, yayin da ake ci gaba da bincike.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai