Ranar ’Yanci: Za A Gudanar Da Addu’o’i Maimakon Bikin A Borno
Gwamnatin Jihar Borno ta ce za ta taikaita bikin zagayowar Ranar Samun ’Yancin Kai Najeriya na bana zuwa addu’o’i.
Gwamnatin Jihar Borno ta ce za ta taikaita bikin zagayowar Ranar Samun ’Yancin Kai Najeriya na bana zuwa addu’o’i.
Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid na ci gaba da cin karen ta babu babbaka a duniyar kwallon kafa a nahiyar Turai.
Kwamitin zaman lafiya na jihar Kano ya yi kira da kada a shiga zanga-zangar tsadar rayuwa irin wadda aka shiga a baya kamar yadda ake raɗe-raɗi.
Al’ummar yankin ƙaramar hukumar Giwa dake Jihar Kaduna na zargin jiragen sojin saman Najeriya da jefa musu bom a masallaci da kuma kasuwa wanda hakan ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 23. Sai dai a nata ɓangaren rundunar sojin sama ta Najeriya ta musanta wannan zargi, ta kuma bayyana cewa harin da ta kai ya tafi […]
Gwamnatin Najeriya ta damƙawa ƙungiyoyin ƙwadago na NLC da TUC da kuma ƙungiyar ɗalibai ta NANS motocin bas masu amfani da iskar gas guda 64 a jiya Lahadi, 29 ga Satumbar 2024. Bikin bada motocin ya gudana ne a fadar gwamantin tarayya da ke Abuja, duka cikin bikin cika shekara 64 da samunƴancin ƙasar. Kashi […]
Gwamnatin tarayya ta bakin Ministan wutar lantarki Mista Adebayo Adelabu, ta bayyana cewa kaso 40 na ƴan Najeriya na samun wutar lantarki ta aƙalla awa 20 a kullum. Ministan ya yi wannan bayani ne yayin wani taro da aka yi duba akan nasarorin da ma’aikatar wutar lantarki ta samu cikin wannan shekara. A cikin wata […]
Shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya naɗa shugabannin sabuwar Hukumar Raya yankin Arewa-maso-yammacin Najeriya. Bola Ahmad Tinubu ya miƙa wa Majalisar Dattawa sunayen shugabannin sabuwar Hukumar Raya Yankin Arewa-maso-yamma domin samun sahalewarsu. Wannan na zuwa ne bayan sanya hannu kan dokar da ta kafa hukumar da shugaban ƙasa ya yi a ranar 24 ga watan […]
Asusun Tallafa Wa Ƙananan Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNICEF) ya ce bai wa yara abinci mai gina jiki cikin kwanakin dubu 1000 na farko bayan haihuwarsu na taimakawa matuƙa wajen bunƙasar ƙwaƙwalwa da haɓakar giraman jikinsu. Jami’ar kula da ingantaccen abinci kuma wakiliyar UNICEF a Kano, Abigail Nyam, ce ta bayyana hakan a ranar […]
Wani rahoto da Hukumar ƙididdiga ta ƙasar Argentina ta fitar na nuni da cewa rabin mutanen ƙasar na fama da matsanancin Talauci. Wannan na bayyana cewa an sami ƙaruwar talauci da kaso 40% cikin 100% na shekarar da ta gabata, kuma ya nuna tasirin matakan tsuke bakin aljihu da gwamnatin shugaban Ƙasar Javier Millei ta […]
Asussun Tallafawa ƙananan yara na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNICEF) na gudanar da taron wayar da kai na kwana biyu da wakilan kafafan yaɗa labarai na jahohin Kano da Jigawa da kuma Katsina a jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya a jihar Kaduna, da nufin samar da hanyoyin ƙarfafa muryar yara domin mahukunta su ɗau matakan […]