Labarai

Kwankwaso da Dickson sun gana kan rikicin NDC a Kano

Ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya gana da Jagoran Jam’iyyar na ƙasa, Sanata Seriake Dickson, a gidansa da ke Guzape a Abuja ranar Talata. Taron ya samu halartar ɗan takarar gwamnan Kano na jam’iyyar, Kwamared Aminu Abdussalam, da Shehu Wada Sagagi, Nasiru Garo da sauran manyan jagororin NDC. […]

Read more

Sojoji sun ceto mutane 47 da ISWAP ta yi garkuwa da su a Borno

Rundunar haɗin gwiwa ta sojojin Najeriya a Arewa maso Gabas, wato Operation Hadin Kai, ta ce ta ceto mutane sama da 47, akasarinsu mata da yara, daga hannun ‘yan ta’addan ISWAP a jihar Borno. Jami’in yaɗa labaran rundunar, Kyaftin Mohammed Goni, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Talata a Maiduguri. […]

Read more

Mutane sama da 1,000 sun kamu a da cutar Ebola a Congo

Cutar Ebola ta kama sama da mutane dubu daya a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo, yayin da barkewar cutar ta bazu zuwa sansanin ‘yan gudun hijira na uku, sannan ta yi sanadin mutuwar wata yarinya yar kimanin watanni 18. Gwamnatin Kongo ta tabbatar da cewa adadin mutanen da suka mutu ya kai 254. Yaduwar cutar cikin sauri […]

Read more